Mazauna garin Janjala da ke yankin Kagarko a jihar Kaduna, sun ce wasu sojoji sun isa garinsu a ranar Talata inda suka kama basaraken kauyen da wasu mazauna kauyen su 10.
Da suke zantawa da jaridar Daily Trust, mazauna garin sun ce kamen ya biyo bayan kama wasu mutane biyu ne a garin Kagarko wadanda ake zargin sun bayar da bayanai wadanda suka kai ga cafke basaraken da sauran mazauna garin.
Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa Daily Trust cewa wadanda aka kaman ana zarginsu da hada baki da ‘yan bindigar da suka addabi mutanen yankin a kwanan nan.
Ya ce an fara kama wasu mutane biyu ne a Kagarko daga nan ne sojoji suka taho cikin motoci kirar Hilux guda takwas zuwa garin Janjala inda suka kama basaraken kauyen da wasu 10.
A Wata majiya ta bakin Yahuza Sulaiman ta ce an tafi da basaraken kauyen Ibrahim Aliyu zuwa babban birnin jihar Kaduna domin ci gaba da bincike.