Duk da tabbacin da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar na cewa, gwamnatin tarayya ba za ta ci gaba da biyan kudin tallafin man fetur ba, amma wani bincike da jaridar Daily Trust ta gudanar, ta gano cewa, gwamnatin ta biya kudin tallafin man fetur Naira biliyan 169.4 a watan Agustan 2023 domin dakile ci gaba da tabarbarewar farashin ferur daga Naira N620 kan kowace lita.
A cikin wata mukala daga kwamitin asusun raba daidai na gwamnatin tarayya (FAAC) wanda kuma jaridar ta gani ta nuna cewa, a watan Agustan 2023, kamfanin iskar Gas na NLNG, ya biya kamfanin NNPC dala miliyan 275.
Kazalika, kamfanin na NNPC ya yi amfani da dala miliyan 220 wanda wannan kudin ya yi daidai da Naira biliyan 169.4 akan Naira 770 duk dala daya, wanda daga ciki, aka yi amfani da dala miliyan 275 don biyan kudin tallafin na mai, inda NNPC, ta haramtacciyar hanya ta rike dala miliyan 55.
Bisa wannan mukalar ta FAAC, hakan ya nuna cewa, biyan tallafin na man fetur ya sake dawo wa, ganin cewa, NNPC na biyan NLNG wasu kason kudade a matsayin tallafin kudin mai.
A cewar masana’antar mai da sarrafa iskar Gas, rahotannin da hukumar NEITI ta gudanar sun nuna cewa, yawan kudin na tallafin man daga 2015 zuwa 2020 sun kai Naira tiriliyan 1.99.
Kazalika, rahotannin da NNPC ta turawa kwamitin FAAC sun nuna cewa, yawan kudin na tallafin man sun kai Naira tiriliyan 1.57 a 2021 sai kuma wasu kudin Naira tiriliyan 1.27 daga watan Janairu zuwa watan Mayun 2022.
Binciken da Daily Trust ta gudanar, ta gano cewa, gwamnatin ta biyan kudin tallafin ne don a ci gaba da daidaita farashin man da a yanzu ake cin gajiyarsa a kasar nan.