Hukumar yaki da cutuka masu yaduwa ta Afirka ta ayyana kyandar Biri a matsayin cuta mai matukar hadari a nahiyar, bayan bullar sabon nau’incutar da ke yaduwa cikin sauri.
Cutar na kara yaduwa cikin sauri a bana, tun bayan da aka fara samun wanda ya kamu da ita a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo.
- Ministocin Wajen Ƙasashen Larabawa Sun Buƙaci Isra’ila Ta Fice Gaba Ɗaya Daga Gaza
- ‘Yan Bindiga Sun Sace Matafiya A Babbar Hanyar Gusau-Funtua
Cibiyar ta yi gargadi kan yadda cutar za ta iya yaduwa sosai idan har aka gaza daukar kwararan matakai.
An dai riga an fargar da likitoci game da yadda sabon nau’in cutar ta kyandar biri ke yaduwa cikin saurin.
Cutar na yaduwa ne a tsakanin mutanen da suka yi cudanya, kuma tana da alamomi masu kama da na mura, sai dai na kyandar biri ya fi tsanani.
A Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo, inda cutar ke yaduwa sosai, mutum 27,000 aka tabbatar sun kamu da ita a bara, daga cikin su kuma fiye da dubu sun mutu.
Cutar ta kuma yadu zuwa kasashe da suka hada da Kenya da Rwanda da Burundi da kuma jamhuriyar Afirka ta tsakiya.
Ana dai sa ran cewa ayyana dokar ta baci a kan kyandar biri zai taimakawa gwamnatoci wajen tsara ayyukan gaggawa domin kai dauki, dakuma kara inganta hanyar shigar da tallafin magunguna a wuraren da aka samu bulluar ta.
Cibiyoyin kula da lafiya a wajen Afirka ma za su sanya ido a kan yadda lamarin zai kasance, da kuma hasashen abin da zai faru nan gaba.
Mece ce cutar kyandar biri, kuma me ke jawo ta?
Cutar kyandar biri wato Mpod, wata kwayar cuta ce ke haifar da ita da ake kira da monkeypod.
Ta na daga cikin nau’ikun cutuka irin na cutar farankama, kodayake ita farankama bata illa kamar Mpod.
Kwayar cutar na ta samo asali ne daga dabbobi inda ta ke yaduwa zuwa bil adama, to amma yanzu abin ya zarta hakan.
An fi samun cutar a kauyukan da ke kusa da manyan dazuka a Afirka, misali kamar a kasashe irinsu Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo.
A irin wadanna yankuna, akwai daruruwan mutanen da suka kamu da wannan cuta har ma da wanda suka mutu ciki har da yara ‘yan kasa da shekara 15wanda su tafi shafa.
Nau’in farko shi ne mai suna “Clade 1” ya fi yaduwa a tsakiyar Afirka. Sai nau’i na biyu na cutar kuma shi ne “Clade 1b”, wato shi ne sabonnau’in cutar mai matukar hadari da ya kuma ya janyo kara yaduwar cutar a yanzu.
Cibiyar CDC, ta ce akwai an samu mutum 14, 500 da suka kamu da cutar kyandar biri, sannan akwai mutum fiye da 450 da suka mutu sakamakon cutar a tsakanin farkon shekarar 2024 zuw watan Yuli na shekarar.
Hakan ya nuna cewa an samu karuwa da kashi 160 ciki 100 na masu cutar, sannan wadanda suka mutu kuma sun karu da kashi 19 ciki 100 idan akakwatanta da irin lokacin a shekarar 2023.
Yayin da kashi 96 cikin 100 na wadanda suka kamu da cutar ta kyandar biri ke a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, cutar na yaduwa zuwa kasashemalwabta kamar Burundi da Kenya da Rwanda da kuma Uganda.
Wani nau’in cutar marar illa sosai da ake kira ” Clade ll” na yaduwa a kasashen yammacin Afirka, wadda ta barke a 2022.
Ita wannan nau’in cuta ta yadu a kusan kasashe 100 ciki har da wasu a Turai da Asiya, inda da wuya a samu cutar, to amma an shawo kanta tahanyar yi wa wadanda ke da yiwuwar kamuwa da cutar allurar rigakafi.
Akwai karancin allurar rigakafin cutar kyandar biri da magungunanta a Congo, sannan kuma jami’an lafiya a kasar na nuna matukar damuwa a gameda yaduwar cutar.
Mene ne alamomin cutar kyandar biri?
Alamomin farko sun hadar da zazzabi da ciwon kai da kumburi da ciwon baya da kuma ciwon gabobi.
Idan aka fara zazzabi, sai kuraje su fito a fuska daga nan sai su yadu zuwa sassan jikin mutum yawanci tafin hannu da kuma tafin kafa.
Kurajen wanda ke da kaikayi sosai ko kuma zafi, na sauyawa a hankali su zama maruru, daga na sai su fashe.
Kurajen na zama a jikin mutum tsawon makonni biyu ko uku, daga nan sai su washe.
To amma idan cutar ta yi tsanani kurajen kan yadu zuwa dukkan jikin mutum musamman baki da idanu da kuma gaban mutum.
Ta yaya cutar ke yaduwa?
Cutar kyandar biri na yaduwa tsakanin mutum da mutum ta hanyar hada jiki da wanda ke da ita ciki har da ta hanyar jima’i da numfashi da kuma sumbata.
Sannan ana daukar cutar ta hanyar taba abubuwa da mai cutar ya yi amfani da su kamar zanin gado da kayan sawa da ma tawul.
Sannan mu’amala da dabbobin da ke da cutar kamar biri da bera da kuma kurege ma na sanya wa a kamu da cutar.
A lokacin da aka samu barkewar cutar a 2022, yawanci cutar ta yadu ne ta hanyar jima’i.
Yaduwar cutar da aka samu ma a yanzu a Congo ana alakanta ne da ta hanyar jima’i.
Yawanci ana samun cutar ne a tsakanin mutanen da suke yawan jima’i da kuma zaman da ke neman ‘yan uwansu maza. Mutanen da ke jima’i da mutane da dama sun fi hadarin kamuwa da cutar.
To amma duk wanda ya yi alaka da wanda ke da alamomin cutar ma zai iya kamuwa da ita ciki har da jami’an lafiya da kuma iyalan mutum.
Shawara ita ce a rinka kaucewa alaka ta kut da kut da duk wanda ke da cutar, sannan a rinka wanke hannaye da sabulu da ruwa idan akwai cutar a gida ko unguwa ko kuma garin da aka samu bullar cutar ta kyandar biri.
Abu na biyu kuma ga wadanda ke da cutar to su killace kansu daga shiga mutane har sai sun warke.
Sannan ga wanda ya warke daga cutar idan zai yi jima’i to ya yi rinka amfani da kororon roba har sai ya yi makonni 12 da warkewa, in ji Hukumar Lafiya ta Duniya.
Za a iya amfani da hanyar da ake bi wajen magance cutar farankama domin maganin cutar kyandar biri, to amma ba lallai a warke ba.
Za iya shawo kan barkewar cutar kyandar biri ta hanyar yaduwar cutar musamman yin rigakafi. Akwai alluran rigakafi uku da ake yi, to amma ana yi wa mutanen da ke da yiwuwar kamuwa da cutar ne rigakafin ko kuma wacanda suka yi alaka ta kut da masu cutar.
Har yanzu Hukumar Lafiya ta Duniya ba ta bayar da shawarar a yi wa kowa rigakafin ba.
A baya-bayannan Hukumar Lafiya ta Duniya ta bukaci masu yin magunguna da su kara samar da rigakafin cutar saboda amfanin gaggawa, koda kuwa alluran rigakafin kasashe ba su amince da su ba a hukumance.