An fara bayar da hidimomin da suka shafi sauka da tashi a birnin Chengdu, ga masu halartar gasar wasanni ta duniya ta Chengdu karo na 12.
Daga sanyin safiyar yau Lahadi, cibiyar tantance masu halartar gasar ta fara aiki a hukumance, inda ta kaddamar da bayar da hidimomin saukaka sauka da tashi ga mahalarta.
- Gwamnatin Katsina Ta Gabatar Da Matsayarta A Taron Jin Ra’ayiyin Jama’a
- ADC Ta Yi Allah-wadai Da Rufe Gidan Rediyon Badeggi FM A Neja
Jirgi mai lamba 3U3920 ya sauka a filin jirgin sama na kasa da kasa na Tianfu na Chengdu da sanyin safiyar yau Lahadi, da tawagar ’yan wasan floorball 30 na kasar Singapore. Kuma su ne tawagar ’yan wasa ta farko da ta sauka a birnin Chendu na lardin Sichuan da ke kudu maso yammacin Sin domin gasar.
Cibiyar tantance mahalarta gasar ta kafa wuraren bayar da hidimomin sauka da fita daga filin jirgin sama na kasa da kasa na Chengdu Tianfu da na Chengdu Shuangliu da tashar jirgin kasa ta Gabashin Chengdu domin masu tambayoyi da neman jagoranci da sauran hidimomi.
’Yar wasan floorball ta kasar Singapore Ong Swee Ling dake ziyartar Chengdu a karon farko, ta ce ayyukan kwastam da na daukar kaya a filin jirgin saman sun gudana cikin sauki kuma ba tare da tangarda ba. Tana fatan za ta taka rawar gani a gasar ta duniya tare da jin dadin zama a Chengdu cikin ’yan kwanaki masu zuwa.
Hidimomin sauka da tashi domin gasar wasanni ta duniya ta Chengdu, za su gudana ne har zuwa ranar 18 ga watan Agusta, inda ake sa ran jami’ai masu alaka da wasanni sama da 5000 ne za su samu sahalewar kwastam a lokacin. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp