Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta fara gudanar da bincike kan mutuwar jami’in kwastam da ake zargin ya kashe kansa ta hanyar harbin kansa da bindiga da kuma mutuwar wasu matasa biyu a unguwar Darmanawa da ke jihar.
Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar.
- Gwamnatin Nijeriya Ta Kafa Makarantar Bayar Da Horo Kan Al’adun Ƙasa – NICO
- Gwamna Nasir Zai Gina Filin Wasan Ƙwallon Guragu A Birnin Kebbi
Abubuwan da suka faru sun haifar da fargaba a tsakanin al’ummar yankin, inda aka dauki matakin gaggawa daga jami’an tsaro.
“Tun da farko dai, kisan kai na jami’in kwastam CSC Abdullahi Abdulwahab Magaji ya haifar da alamomin tambayoyi, lamarin da ya sa ‘yansandan gudanar da bincike mai zurfi.” in ji sanarwar.
Rundunar ta ce ba za ta yi kasa a gwiwa ba har sai ta tabbatar da gaskiyar lamarin, tare da bayyana wa al’umma abin da ya faru.