Ministan Kudi kuma Ministan Tattalin Arziki, Wale Edun, ya bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da binciken kwakwaf akan asusun kamfanin man fetur na Nijeriya (NNPCL) domin inganta tsarin yadda kamfanin ke hada-hadar kudaden shigarsa.
Edun, a yayin da yake jawabi a taron zuba jari na Nijeriya da aka gudanar a birnin Washington DC na Amurka, ya ce gwamnatin tarayya na kokarin daidaita litattafan asusun ajiyarta, inda ya kara da cewa, kamfanin NNPCL na sa ran zai samar da karin kudaden shiga na musayar kudin waje ga asusun gwamnati.
- Ministan Harkokin Wajen Kasar Sin Ya Yi Kira Ga Sin Da Birtaniya Da Su Kiyaye Tsarin Kasa Da Kasa Da Aka Kafa Bayan Yakin Duniya Na Biyu
- Shawarar Tabbatar Da Tsaro A Duniya Ta Samar Da “Kyakkyawan Fata” Ga Duniya Mai Fama Da Tashin Hankali
Edun ya yi karin haske da cewa, ana gudanar da binciken kwakwaf ne ga NNPCL domin fahimtar yadda kamfanin ya yi hada-hadar kudade a baya kafin cire tallafin man fetur da kuma bayan cire tallafin, “Akan bashin da ake bin NNPC….Ana ci gaba da binciken NNPC, domin mu fahimci hakikanin abin da ya faru a baya.
“Akwai wasu bincike da ake gudanarwa domin kamar yadda muka sani, an sanar da cire tallafin man fetur ne a ranar 29 ga watan Mayun 2023, amma an dauki lokaci kafin a cimma wannan kudurin. A halin yanzu, wani bangare na biyan basussukan da ake bin NNPC, daga kasafin kudin gwamnati ake tanada”.
Ya kara da cewa, babban aikin da ke gaban NNPCL shi ne bunkasa hako danyen mai da kuma samar da karin kudaden shiga – a takardun Dala zuwa Asusun Tarayya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp