Majalisar wakilai ta umarci kwamitocin sadarwa da harkokin cikin gida da su binciki haɗa lambar shaidar zama ɗan ƙasa (NIN) da layukan waya ba tare da izini ba da kamfanonin sadarwa ke yi.
Wannan mataki ya biyo bayan ƙudirin da ‘yan majalisa Patrick Umoh da Julius Ihonvbere suka gabatar, inda aka buƙaci hukumar NCC ta ɗauki mataki kan duk wani kamfanin sadarwa da aka samu da laifi, tare da NIMC ta tabbatar da sahihancin haɗa bayanan NIN.
- Ana Shirin Kiranye Ga Ɗan Majalisar Da Ya Bar Kwankwasiyya
- Trump Ya Hana Maza Masu Sauyin Jinsi Shiga Wasannin Mata
Umoh ya ce wannan mataki na iya haifar da damuwa ga ‘yan ƙasa, tare da jefa su cikin hatsarin satar bayanai, da damfara, da wasu laifukan intanet. Kwamitin binciken na da makonni huɗu domin kammala aikinsa.