Kamfanin hakar albarkatun mai na teku mallakin kasar Sin ko CNOOC a takaice, ya ce an kaddamar da aikin ginin sashe na 2, na rijiyoyin hakar iskar gas na cikin teku mai zurfi, a yankin hakar albarkatun iskar gas na Shenhai Yihao.Â
Aikin wanda kasar Sin ke jagorantar aiwatar da shi bisa fasahohin kashin kan ta, za a gudanar da sashen sa na 2 ne cikin tekun dake da nisan kilomita 200 daga gabar teku a birnin Sanya na lardin Hainan dake kudancin kasar Sin. Ana kuma sa ran bayan kammalar sashen na 2, za a samu karin adadin iskar gas da ake hakowa a yankin na Shenhai Yihao, daga kyubik mita biliyan 100, zuwa kyubik mita biliyan 150.
Kamfanin CNOOC ya ce a sashen aikin na 2, ana fatan haka rijiyoyin iskar gas 12, wadanda za su ba da damar fadada adadin iskar gas da ake hakowa duk shekara a yankin zuwa kyubik mita biliyan 4.5, adadin da zai kai kaso 90 bisa dari, na adadin iskar gas din da lardin Hainan ya yi amfani da shi a shekarar 2021 da ta gabata.
Da yake karin haske kan hakan, babban injiniyar kamfanin CNOOC reshen Hainan Liu Shujie, ya ce, zurfin wurin da za a haka zai kai mita sama da 60,000, adadin da zai zarta zurfin sashen farko na aikin da aka kammala da kaso 220 bisa dari, wanda kuma shi ne mafi zurfi idan an kwatanta da makamantan sa dake sauran sassan duniya.
Yankin farko na hakar iskar gas a cikin teku mai zurfi na Shenhai Yihao, ya fara aiki ne a watan Yunin shekarar 2021, shi ne kuma yankin hakar iskar gas irin sa mafi zurfi a dukkanin kasar Sin. (Saminu Alhassan)