Da sanyin safiyar yau, 14 ga watan, an fara sufurin kayayyakin jin kai na shawo kan bala’in girgizar kasa da gwamnati ta Sin ta bai wa Sham. An yi hasashe cewa, za su isar da su Damascus na kasar Sham gobe da safe.
Wadannan kayayyakin jin kai sun kunshi kunsoshin ceto na gaggawa guda dubu 30, da rigunan maganin sanyi dubu 10, da tantuna guda 300, da barguna dubu 20 da wasu na’urorin numfushi da injunan sa barci, da na’urorin samar da iskar oxygen, da wasu fitilolin tiyata marasa inuwa na LED da dai sauransu.
Bugu da kari, an isar da wasu kayayyakin jin kai da kungiyar Red Cross ta Sin ta bai wa kasar Sham karo na biyu Damascus, fadar mulkin kasar Sham a jiya Litinin. Jakadan Sin dake Sham Shi Hongwei, da mataimakin ministan ma’aikatar kula da harkokin wurare da muhalli na kasar Sham Muataz da sauransu sun je filin jirgin sama don karbarsu.
An labarta cewa, wadannan kayayyaki sun kunshi tantuna, jakunan ceto na gaggawa, tufafi da magunguna da sauran abubuwan da ake bukata cikin gaggawa a inda bala’in girgizar kasa ta shafa. Wadannan kayayyaki za su iya taimakawa masu fama da bala’in fiye da dubu 10.
Bisa wani labara daban da aka bayar, an ce, ya zuwa ranar 12 ga wata, tawagar ceto ta kasar Sin ta ta riga ta ceci mutane shida a cikin yankunan birnin Antakya dake lardin Hatay na kasar Turkiyya da bala’in ya shafa.
Kawo yanzu,kungiyar ceto ta Sin ta riga ta aika kananan tawagogin ceto har sau 13, tare da ma’aikatan ceto 206. Sannan sun ceci mutane guda 6, da kuma samun gawawwaki 8 wadanda suka rasa rayukansu cikin bala’ain. Ban da wannan, tawagar ceto ta Hongkong ta Sin ma ta ceci mutane 3 a Turkiyya. (Safiyah Ma)