A yau Laraba ne aka bude dandalin taron Nishan game da wayewar kai a duniya karo na 11 a birnin Qufu da ke lardin Shandong na gabashin kasar Sin. Taron wanda ya dauki tsawon kwanaki biyu ana gudanarwa, ya tattaro masana na duniya wuri guda domin yin nazari kan mu’amala a tsakanin mabambantan al’adu da kuma zamanantarwa.
Taron dandalin na bana, mai taken “Kyawun da ke cikin Bambance-bambance: Raya fahimtar juna tsakanin wayewar kai daban-daban don zamanantar da duniya,” ya jaddada kudurin kasar Sin na kiyaye mabambantan al’adun bil’adama, tare da sa kaimi ga ci gaban duniya cikin lumana.
Sama da baki 500 ne suka halarci taron, ciki har da kusan mahalarta 300 daga sassan kasa da kasa wadanda suka fito daga kasashe fiye da 70. Kazalika, wadanda suka halarci taron sun hada da manyan kusoshi daga kasashen waje, da wakilan kungiyoyin kasa da kasa, da jakadun kasashe a kasar Sin da kuma kwararrun duniya.
An sanya wa dandalin tattaunawa na Nishan sunansa ne daga dutsen Nishan mai nisan kimanin kilomita 30 daga kudu maso gabashin Qufu. Har ila yau, dandalin wanda ya samo asali daga mahaifar babban malami masanin falsafar kasar Sin, Confucius, ya zama wani muhimmin fage na fahimtar kasar Sin, da karfafa cudanyar al’adu, da cimma matsaya game da wayewar kai a duniya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp