A yau ne, aka yi bikin gabatar da bidiyon musamman na bayanin magabata da shugaba Xi Jinping yake so, cikin harshen Indonesia da na Thailand, da kuma bidiyo mai taken Sin ta kama sabuwar hanyar neman samun ci gaba, cikin harsuna daban daban a nan birnin Beijing, inda shugaban babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG Shen Haixiong ya halarci bikin tare da gabatar da jawabi. Kana shugabannin gidajen telebijin na kasashe da dama ciki har da Indonesia da Thailand da Indiya da Nijeriya da sauransu sun halarci bikin ta hanyar yanar gizo.
Cikin jawabinsa, Shen Haixiong ya ce, CMG da gidajen telebijin na kasashe 8 sun yi hadin gwiwa wajen daukar bidiyo mai taken Sin ta kama sabuwar hanyar neman samun ci gaba, wanda za a yi amfani da wasu labarai masu ban sha’awa don masu kallo na kasashen waje su fahimci yadda Sin take kokarin zamanintar da kanta bisa irin nata salo, kana zai shaida dalilin da ya sa Sin ta samu nasarori.
Ya ce CMG yana son kara yin kokari tare da kafofin watsa labaru na kasa da kasa, wajen kirkiro tsarin hadin gwiwa, da inganta hadin gwiwa, da kuma fadada fannonin hadin gwiwa don samar da gudummawa wajen samun zaman lafiya da bunkasuwa a duniya, da kuma raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil’adama. (Zainab)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp