Albarkacin ziyarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping zai yi a birnin Rio de Janeiro na kasar Brazil, don halartar taron rikon kwaryar shugabannin G20 karo na 19, babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin, wato CMG a takaice ya shirya wani bikin baje kolin nagartattun shirye-shiryensa a birnin São Paulo na kasar Brazil, inda ya gabatar da shirye-shiryen talibijin masu dadin kallo fiye da 20, a kafofin yada labarai fiye da 10 dake kasar, ciki har da shirin “Gamuwa da Xi Jinping”.
Shugaban CMG Shen Haixiong ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo, inda ya ce CMG da hadin gwiwar kafofin yada labarai na kasar Brazil ne suka shirya gabatar da wannan biki, kuma hakan mataki ne na kara cudanyar al’adun kasashen biyu, da kara dankon zumuncin al’ummunsu. (Amina Xu)