Tun a shekarar 2008, kungiyar ingiza cinikayyar Sin ta kan gabatar da rahoton binciken kamfanonin Sin game da halinsu na zuba jari a ketare, da kuma burinsu a wannan fanni. Kana a gun taron manema labaran da aka yi a yau Juma’a, an gabatar da rahoton shekarar bara.
Rahoton ya nuna cewa, a shekarar bara, kamfanonin Sin sun zuba jari a ketare yadda ya kamata, inda kashi 80% daga cikin wadannan kamfanoni suka habaka ko kiyaye yawan kudaden da suka zuba a ketare, wanda ya karu da kashi 10% bisa na 2022, kana yawan kamfanoni fiye da kashi 90% sun amince da makomar zuba jari a ketare.
Ban da wannan kuma, yawan kamfanoni da ya kai kaso 70% sun zabi kasashe dake halartar tsarin shawarar “ziri daya da hanya daya”. A halin yanzu, kamfanoni fiye da kashi 60% sun zuba jari a waje don habaka kasuwar ketare. Kaza lika, yawan ribar da kamfanonin suka samu ta hanyar zuba jari a ketare ya karu ko ta gudana bisa daidaito. Kana yayin da ake zuba jari, kaso 60% na kamfanonin suna la’akari da yin amfani da kudin Sin RMB. (Amina Xu)