ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, June 27, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Zulum Ya Ba Da Tallafin Fetur Ga Manoma Don Habbaka Noman Rani

by Sani Anwar
2 years ago
zulum

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya biya tallafin man fetur domin a sayar wa manoma kowace lita a kan Naira 500 maimakon 730 a Jihar Borno.
Manoman da za su ci gajiyar tallafin su ne na Damasak, da ke Arewacin jihar; don kara habbaka noman rani.

Kazalika, gwamnan ya kaddamar da tashar samar da ruwan sha mai karfin dawakai 90 duk dai a garin na Damasak, a lokacin ya kai ziyarar aiki garin.

  • Gwamnan Bauchi Ya Biya Kashi 50 Na Karin Kudin Kujera Ga Alhazan 1652
  • Zulum Ya Rabawa ‘Yan Sa Kai Da Mafarauta 5,523 Naira Miliyan 255 Da Buhunan Shinkafa 5,513

Wannan tasha ta samar da ruwan sha mai dauke da karfin dawakai 90, an tanadar mata hasken wuta na sola mai amfani da hasken rana mai karfin nauyin kilowatt 115, domin yin ban ruwa ga wasu bangarori guda uku tare da samar da adadin ruwan da ya doshi lita 225 a duk dakika daya da kuma fitar maki 105, wanda ya kunshi kadada 125 na wurin noman shinkafa.

ADVERTISEMENT

Zulum ya sanar da cewa, gwamnatinsa za ta sauya akalarta ne daga ci gaba da rabon kayan abinci ga al’ummarta zuwa karfafa wa manoma guiwa tare da ba su dukkanin gudunmawar da ta dace, domin inganta harkokin noma a fadin jihar.

“Magance matsalolinmu na dan kankanin lokaci, ba zai taba dawwama ba, sannan ci gaba da yin rabon kayan abinci ga mutane, musamman ‘yan gudun hijira wadanda suke zaune a sansaninsu, shi ma ba zai taba dorewa ba. Don haka, babu abin day a fi dacewa da mu; illa mu canza tinaninmu daga magance matsalolinmu na dan kankanin lokaci zuwa na tsawon lokaci, wanda shi ne kadai masalaha a gare mu; wannan kuwa ba wani abu ba ne illa NOMA,” in ji Zulum.

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Ta Raba Wa Manoma 2,930 Buhun Taki 11,720 A Abuja

Ku Gaggauta Fara Yin Shuka A Kakar Bana: Saƙon Hukumar NiMet Ga Manoma

Har ila yau, ya bayyana aniyarsa ta samar da man fetir kimanin lita miliyan daya ga manoma, wanda a cewar tasa za a rarraba shi zuwa kowace karamar hukuma da ke fadin jihar.

Zulum
Sani Anwar
+ postsBio
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Tattalin Arziƙin Ƙasa: Masana Sun Buƙaci Tinubu Ya Yi Hattara Da Shawarar IMF
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Cututtukan Da Aka Fi Fama Da Su Lokacin Damina Da Yadda Za A Kauce Musu (2)
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Cututtukan Da Aka Fi Fama Da Su Lokacin Damina Da Yadda Za A Kauce Musu (1)
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Talauci Ya Sake Karuwa Da Kashi 63 Duk Da Sauye-sauyen Tattalin Arzikin Da Gwamnati Ta Yi – IMF

MASU ALAKA

Gombe Ta Zabge Farashin Taki Da Kashi 50 Cikin 100
Noma Da Kiwo

Gwamnatin Tarayya Ta Raba Wa Manoma 2,930 Buhun Taki 11,720 A Abuja

June 27, 2026
Zulum
Noma Da Kiwo

Ku Gaggauta Fara Yin Shuka A Kakar Bana: Saƙon Hukumar NiMet Ga Manoma

June 27, 2026
Zulum
Noma Da Kiwo

Dalilin Gwamnatin Tarayya Na Fara Aikin Gina Mayankar Zamani A Garin Jos

June 26, 2026
Next Post
Jimilar Kudin Da Sin Ta Samu Wajen Jigilar Kayayyaki A Farkon Watanni Biyu Na Bana Ta Kai Yuan Triliyan 55.4

Jimilar Kudin Da Sin Ta Samu Wajen Jigilar Kayayyaki A Farkon Watanni Biyu Na Bana Ta Kai Yuan Triliyan 55.4

LABARAI MASU NASABA

Zaben 2027: Jam’iyyun Siyasa Sun Bayyana Shirinsu Yayin Da INEC Ta Fitar Da Jawalin Zabe

2027: Jam’iyyun Siyasa Sun Yi Maraba Da Hukuncin Kotu Kan Dakatar Da Jadawalin INEC

June 27, 2026
ADC Ta Yi Allah-Wadai Da Soke Rajistar NDC, Ta Yi Gargaɗi Kan Barazanar Dimokuraɗiyya

ADC Ta Yi Allah-Wadai Da Soke Rajistar NDC, Ta Yi Gargaɗi Kan Barazanar Dimokuraɗiyya

June 27, 2026
TCN Ta Sanar Da Ɗaukewar Wutar Lantarki A Kano Da Wasu Jihohi Huɗu

TCN Ta Sanar Da Ɗaukewar Wutar Lantarki A Kano Da Wasu Jihohi Huɗu

June 27, 2026
Magoya Bayan Pantami Sun Zargi Ana Musgunawa Gombawa Motors A Gombe

Magoya Bayan Pantami Sun Zargi Ana Musgunawa Gombawa Motors A Gombe

June 27, 2026
Babu Wani Saɓani Tsakanin Osimhen Da Lookman – Ndidi

Babu Wani Saɓani Tsakanin Osimhen Da Lookman – Ndidi

June 27, 2026
Gasar Kofin Duniya: Senegal Ta Kai Zagaye Na 32 Bayan Lallasa Iraki Da Ci 5-0

Gasar Kofin Duniya: Senegal Ta Kai Zagaye Na 32 Bayan Lallasa Iraki Da Ci 5-0

June 27, 2026
Tinubu Ya Sanya Hannu Kan Sabuwar Dokar Shaidar Ɗan Ƙasa, Duba Abin Da Ta Ƙunsa

Tinubu Ya Sanya Hannu Kan Sabuwar Dokar Shaidar Ɗan Ƙasa, Duba Abin Da Ta Ƙunsa

June 27, 2026
Zulum

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (1)

June 27, 2026
Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa

An Kama Uwa Da Abokiyar Burminta Kan Kisan Jariri A Jihar Yobe

June 27, 2026
Gombe Ta Zabge Farashin Taki Da Kashi 50 Cikin 100

Gwamnatin Tarayya Ta Raba Wa Manoma 2,930 Buhun Taki 11,720 A Abuja

June 27, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.