Hukumar sauraron korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano (PCACC) ta bankado buhunan shinkafar tallafi 16,800 mai nauyin kilo 50 da aka sauyawa buhu domin sayarwa a wani rumbun ajiyar kayayyaki mai zaman kansa a jihar.
Da yake zantawa da manema labarai a rumbun ajiyar da ke ‘Ring Road’ a Kano a ranar Talata, shugaban hukumar PCACC, Muhyi Magaji, ya ce an gano badakalar ne ta hanyar rahotonnin sirri da ‘yan kasa nagari suka bayar.
- An Bude Bikin Baje Kolin Samar Da Kayayyaki Na Duniya Na Kasar Sin Karo Na Biyu A Beijing Domin Karfafa Hadin Gwiwa
- Gobara Ta Laƙume Kadarorin Nairori A Wata Kasuwa A Legas
Ya zuwa yanzun, hukumar ta kama mutum daya da ke da hannu a lamarin, yayin da za a tsananta bincike domin kamo duk wanda ke da hannu a lamarin.
“Wannan buhunan shinkafar 16,800 an tanade su ne don tallafin azumin watan Ramadan da ya gabata, amma aka karkatar da su zuwa wannan rumbun aka sauya musu buhu domin sayarwa,” in ji shi.
Muhyi ya tabbatar da cewa, buhunan shinkafar kimanin tirela 28 ne yayin da kowacce tirela ke dauke da buhu 600.
Ya kara da cewa shinkafar akwai tambarin sunan shugaban kasa Bola Tinubu kuma an rubuta ‘Not For Sale’, ma’ana “ba ta sayarwa ba ce”.
Amma mutane da karfin hali, sai ga shi an sauya buhun da wani buhun shinkafa mai suna ‘Big Mama Rice Premium Quality’, wasu kuma ‘Elephant Classic Parboiled Rice’.
Muhyi ya bayyana cewa, za a mika dukkan wannan bayanan ga gwamnan jihar, Abba Yusuf, domin daukar matakin da ya dace.