Kwayar cutar bakteriya ta shigella na bazuwa ne ta hanyar taba dagwalon bayan gida
Likitoci sun ce wasu a cikin dakarun sojin Isra’ila da ke fada a mamaye ta kasa a Gaza, suna fama da wani matsanancin ciwon ciki sanadin wata cuta da ake kira “shigella”.
Ana jin cutar na bazuwa ne sakamakon rashin yanayi mai tsafta da kuma abinci maras aminci a fagen yaki.
Likitoci da yawa a Rundunar Sojin Isra’ila sun ba da rahoton bullar matsananciyar cutar ciwon ciki tsakanin dakarun da ke Gaza, a cewar Dakta Tal Brosh, daraktan Sashen Cutuka masu Yaduwa a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Assuta Ashdod.
- Gwamnatin Kano Za Ta Biya Wadanda Ta Yi Wa Rusau Diyyar N3bn
- Hatsarin Jirgin Ruwa Ya Yi Ajalin Mutane 2 A Adamawa
Ya ce ya gano suna fama da cutar da ake kira shigella ne. Sojojin Isra’ila mai yiwuwa sun kamu da cutar shigella ne daga abincin da dangi da abokan arziki ke aika musu
Ana kebe sojojin da suka kamu, sannan a mayar da su gida don yi musu magani.
Dr Broch ya ce “fayyataccen sanadi” guda da ya janyo barkewar cutar shi ne abincin da fararen hula ‘yan Isra’ila suka girka kuma aka aikawa dakaru a Gaza.
Ya ce mai yiwuwa ne abincin ya gurbata da kwayar cutar shigella, da sauran miyagun kwayoyin bakteriya, saboda rashin sanyaya abincin a lokacin da ake tafiya da shi ko kuma rashin dumamawa sosai kafin a ci.
“Da zarar sojoji sun kamu da gudawa, larurorin rashin tsafta masu alaka da fagen yaki kan haddasa yaduwar cutar daga mutum zuwa wani,” ya ce. Dakta Broch ya kara da cewa kamata ya yi a aika wa dakarun soji kayan abincin da kawai aka kyafe kamar abincin gwangwani da nau’o’in biskit da gyada da sauransu, kamar yadda BBC ta labarto.
Shigella nau’in kwayar cutar bakteriya ce. Kuma idan ta shiga cikin jiki, tana janyo wani ciwon ciki mai haddasa kashin jini mai suna “shigellosis”.
Mutanen da ke cikin halin rashin lafiya ko kuma wadanda garkuwar jikinsu ta yi rauni sanadin cutuka kamar cutar kanjamau, na iya jin jiki daga wadannan alamomin cuta tsawon lokaci.
Matukar ba a yi magani ba, cutar shigella na iya kawo tsananin rashin lafiya, kai har ma da mutuwa.
Hatsarin mutuwar musamman, ya fi yawa idan kwayoyin cutar bakteriya suka shiga hanyoyin jini.
A cewar Cibiyar Dakile Cutuka masu Yaduwa ta Amurka, shigella na bazuwa “cikin sauki” ta hanyar hulda kai tsaye ko a kaikaice da bayan gidan mutumin da ya kamu.
Cibiyar Dakile Cutuka masu Yaduwa ta Amurka ta kiyasin cewa ana samun mutane tsakanin miliyan 80 zuwa miliyan 165 da ke kamuwa da cutar duk shekara a fadin duniya, inda take haddasa mutuwar mutum 600,000.