An gano cewa dukiyar da Iyalan Masarautar Saudiyya ke da ita ta kere ta hamshakin mai kudin nan na duniya, mamallakin Kamfanin Manhajar D (twitter) da shugaban kamfanin Microsoft arziki a duniya, inda abin da suke da ita ta kai dalar Amurka tiriliyan 1.4 (Yuro Tiriliyan £1.1).
MujallarForbes ta kiyasta arzikin Elon Musk, mamallakin D a matsayin dala biliyan 251.3 (£ 191bn), yayin da Bill Gates, mai kamfanin Microsoft arzikinsa ya kai dala biliyan 119.6 (£93bn).
- Bankin Duniya Ya Yi Hasashen Bunkasar Tattalin Arzikin Nijeriya Da Kashi 3.3 A 2024
- Za A Kulle Miliyoyin Asusun Banki Saboda Rashin Katin Dan Kasa
Gidan sarautar Saudiyya ya hada da zuriyar Muhammad bin Saud, wanda ya kafa Masarautar a karni na 18.
Iyalan masarautar sun kunshi kusan dangi 15,000 – ko da yake dukiyar masarautar mutum 2000 ne ke juya ta.
Bangaren da ke mulki a masarautar ya fito ne daga zuriyar Abdulaziz bin Abdul Rahman, wanda ya zamantar da Saudiyya.
Shugaban zuri’ar masarautar a yanzu shi ne Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud, wanda hau karagar mulki tun a shekarar 2015.
Fitaccen dansa wanda kuma shi ne magajinsa; Mohammed bin Salman, wanda aka fi sani da MBS, Yarima mai jiran gado, wanda kuma shi Firaministan Saudiyya na yanzu wanda da yawa a kasar ke kallon sa a matsayin mai juya akalar mulkin Saudiyya.
MBS da Sarki Salman suna sa ido kan abin da ya shafi tafiyar da masarautar da abin da ya shafi tauye ‘yancin jama’a da ‘yancin siyasa.
Asalin arzikinsu ya samo asali ne daga man fetur da aka samo a kasar shekaru 70 da suka gabata, wato tun a zamanin Sarki Abdulaziz bn Saud.
Masarautar Saudiyya na boye bayanan arzikinsu da yadda suke tafiyar da harkokin kudadensu, amma yadda suke kashe kudade da tafiyar da rayuwarsu ya sanya a lokuta da dama hankalin jama’a ke zuwa kan su.
A halin yanzu, harkokin kudin gidan sarautar Birtaniya na ka terere daga kafofin watsa labarai da jama’a.
Kamfanin Brand Finance ya yi wa dukiyar masarautar da Sarki Charles III ke jagoranta kimar daraja dala biliyan 88 (£69bn).