Bayan kwana shida ana ci gaba da neman gawarta, a ƙarshe an gano gawar yarinya Haneefa, mai shekaru uku, wadda ruwan sama ya tafi da ita a Zariya. An gano gawar ce da safiyar Lahadi, a bayan Gyallesu, ƙasan Kilaco, kamar yadda babban jami’in Red Cross na shiyyar Zariya, Abdulmumin Adamu, ya tabbatar.
A cewarsa, wannan ya kawo ƙarshen binciken neman waɗanda iftila’in ambaliyar ruwan sama ya rutsa da su. A ranar 8 ga Satumba 2025, ruwan sama mai ƙarfi da aka tafka a unguwar Tudun Jukun kusa da Tukur-Tukur ya yi sanadin mutuwar Fatima Sani Danmarke da Yusuf Surajo (wanda aka fi sani da Abba), wanda sun kasance duk ɗalibai ne, tare da janyo ɓacewar Haneefa wadda Fatima ke goye da ita a lokacin.
- Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum Uku A Zariya
- Jam’iyyar APC Ta Lashe Zaɓen Kujerun ‘Yan Majalisun Zariya Da Basawa
Kakan yarinyar, Mallam Suleiman, wanda ke zaune a layin Adamu Mai Aljana, Magume, ya tabbatar da cewa wata bishiya ce ta tare gawar yarinyar a bayan Gyallesu. Ya bayyana cewa an gudanar da Sallar jana’iza nan take bayan gano gawar, duk da cewa tun a jiya aka yi mata Salatul Gaib a masallacin Mallam Isa Cikon Kwami.
Dangin yarinyar, ciki har da Alhaji Sani Danmarke, sun yi godiya ga jama’a bisa jajircewa wajen neman yaran da iftila’in ya shafa, tare da yin addu’ar rahma ga mamatan.
A halin yanzu, limaman masallatai na ci gaba da wayar da kan al’umma kan matakan kariya, suna jan hankalin iyaye da masu ababen hawa su yi hattara yayin ruwan sama mai ƙarfi, don guje wa maimaituwar irin wannan masifa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp