Gwamnatin jihar Kano ta gano wata ma’ajiya da ake ajiye gurbataccen taki a Gunduwawa da ke Karamar Hukumar Gabasawa.
Shugaban Hukumar Kare Hakkin Mai Saye ta jihar, Baffa Babba Dan’agundi, ne ya bayyana hakan ta bakin kakakin hukumar, Musbahu Yakasai, a yau Talata a Kano.
- Majalisa Ta Musanta Shirin Tsige Kakakin Majalisar, Femi Gbajabiamila
- Xi Ya Aike Da Sakon Taya Murna Ga Taron Dandalin Tattaunawar Zaman Lafiya Da Tsaro Na Sin Da Afirka Karo Na Biyu
“Mun samu bayanan sirri cewa akwai wani mamallakin ma’ajiyar taki yana hada takin da yashi, sanan ya siyarwa manoma.
“Hakan ya sa muka daumi matakin rufe ma’ajiyar, domin kare al’ummar jihar Kano daga amfani da taki mara kyau.” Inji shi.
Yakasai ya kuma kara da cewa a baya ma hukumar ta kama wata mota cike da garin semovita mara kyau a kasuwar Singa, inda ya kara da cewa hukumar ta kara kama wata ma’ajiyar takin mara kyau a karamar hukumar Garko.
Ya kuma nemi al’umma da su ci gaba da bai wa hukumar bayanan irin wadannan wurare domin kare lafiya da ma rayukan al’ummar jihar.