Hukumar kare hakkin masu sayayya ta Nijeriya (Consumer Protection Commission), ta gano wani nau’in sukari mara inganci, wanda ba a yi wa rajista ba, da ake sayarwa a kasuwannin kasuwanni.
Hukumar ta ce tana kokarin shawo kan lamarin, kamar yadda ta bayyana a wata sanarwa da ta fitar.
- Kasar Sin: Ya Kamata Nahiyar Turai Ta Girmama Manufar Kasar Sin Daya Tak A Duniya
- Sin Tana Fatan Raya Duniya Mai Adalci Dake Samun Bunkasuwa Tare Tsakanin Mabambantan Bangarori
Ta wallafa sanarwar a shafinta na X, inda ta ce sukarin mara ingancin da ta bankado a wasu kasuwannin, wasu kamfanoni ne suka shigo da shi daga kasar Brazil.
Hukumar ta yi nuni cewa an gano sukarin ba ya dauke da sinadarin vitamin A da ake matukar bukata ya kunsa, wanda kuma muhimmin abu ne ga inganta lafiyar ido, da kare garkuwar jiki, da kuma kyautata lafiyar dan Adam.
Wasu bayanan sirri da hukumar ta samu ne suka kai jami’anta ga gudanar da bincike, musamman a yankunan kudu maso yamma da arewa maso gabas.
Binciken ya gano cewa, mafi yawan sukarin da aka tantance ba shi da wata alama da za a iya shaida sahihancinsa, ciki har da rashin kwanan watan da aka sarrafa shi da kuma ranar da zai lalace.
Sukarin kuma ba shi da rajistar hukumar NAFDAC da akan wajabta yi wa kayan abinci da magunguna da na masarufi da dai sauransu.
Hukumar ta ta lashi takobin bin dukkanin matakan da suka dace, wajen ganin ta dakile bazuwar sukarin da ma sauran wasu abubuwa marasa inganci da ake sayarwa a kasuwannin Nijeriya.