A yau Asabar 6 ga wata ne, kamfanin samar da hidimomin watsa shirye-shirye na kwamitin shirya gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta kasa da kasa wato OBS a takaice, da babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin ko kuma CMG a takaice, suka rattaba hannu kan takardar bayani ta hadin-gwiwa a Beijing, inda aka gayyaci CMG, don ya zama babbar kafar watsa labarai a gasar wasannin Olympics wadda za ta gudana a shekara ta 2024 a birnin Paris na kasar Faransa. Kana, bangarorin biyu za su kafa wani tsarin hadin-gwiwa mai dorewa, a wani kokari na tallata ruhin wasannin Olympics.
Shugaban CMG, Shen Haixiong ya bayyana cewa, an gayyaci CMG don ya zama daya daga cikin manyan kafafen yada labaran duniya a yayin gasar wasannin Olympics ta Paris, inda zai samar da siginar talabijin kan wasu manyan gasanni hudu, da tura wata babbar tawagar ma’aikatan watsa labarai sama da dubu 2, gami da yin amfani da fasahohin sadarwar zamani dake kunshe da “5G+4K/8K+AI”, don gabatar da wata kasaitacciyar gasar Olympics ga miliyoyin masu kallo na kasa da kasa. (Murtala Zhang)