An gudanar da bikin kafofin watsa labaru na “Abokan Afirka” mai taken “Yin mu’amalar al’adu da neman cimma buri ta hanyar fasahohin sadarwa” a birnin Beijing, inda memban hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta Sin Li Shulei ya halarta ta kafar bidiyo tare da gabatar da jawabi.
Mahalartar bikin sun bayyana cewa, bisa jagorancin shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugabannin kasashen Afirka, an shiga sabon mataki wajen raya dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka mai inganci da neman makomar bai daya ta Sin da Afirka. Za a gudanar da taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC na shekarar 2024 a birnin Beijing, inda za a bude sabon babi na raya dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka da neman makomar bai daya tare.
- Shugaban Afirka Ta Tsakiya: Karin Kasashen Afirka Suna Son Zurfafa Hadin Gwiwa Da Sin
- An Cafke Mutumin Da Ake Zargi Da Garkuwa Da Almajirai 2 A Bauchi
Kana mahalartar bikin sun yi fatan cewa, bisa yanayin tinkarar sauyi da bunkasuwar fasahohin sadarwa a duniya, ya kamata kafofin watsa labaru na Sin da Afirka su rungumi tunanin yin hadin gwiwa da samun moriyar juna, da yin bayanai kan hadin gwiwa da ci gaban Sin da Afirka yadda ya kamata, don samar da yanayin watsa labaru cikin adalci da dacewa a duniya.
Babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG ya dauki nauyin gudanar da bikin, inda wakilai fiye da 200 daga kungiyoyin kasa da kasa da kafofin watsa labaru da kungiyoyin masana na Sin da kasashen Afirka fiye da 20 suka halarci bikin. (Zainab Zhang)