An gudanar da bikin murnar bikin bazara na shekarar 2023 a birnin Abuja dake Nijeriya, inda aka gwada abincin Sin, da shirye-shiryen nuna fasahohin Sin da Nijeriya, da fasahar dafa shayi na Sin, fasahar yanka takardu ta gargajiya ta Sin, da bikin nune-nunen hotuna game da nasarorin da Sin ta samu a cikin shekaru 10 da suka wuce, da siniman Sin, da bidiyoyi masu kyau na Sin da Nijeriya da sauransu, wadanda suka haskaka bikin sosai.
Ofishin jakadancin Sin dake kasar Nijeriya da cibiyar al’adun Sin dake Nijeriya ne suka dauki bakuncin gudanar da bikin. Mataimakiyar ministan harkokin watsa labaru da al’adu na kasar Nijeriya Lidia Shehu Jafiya da ta yabawa wannan biki, ta bayyana cewa, abinci da al’adun bikin gargajiya su ne muhimman hanyoyin dake samun saukin fahimtar wata kasa, tana fatan kasashen biyu za su kara yin mu’amala da juna ta bukukuwa kamar hakan, da sa kaimi ga hadin gwiwar al’adu a tsakaninsu, ta hakan jama’ar kasashen biyu za su kara fahimtar juna. (Zainab)