A ranar 11 ga watan nan, wato ranar ce ta murnar cika shekaru 52 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Jamus, babban rukunin gidan rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG, ya gabatar da bikin mu’ammalar al’adu don murnar cika shekaru 10 da kulla huldar abota bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni tsakanin kasashen biyu, bisa jigon “Samun ci gaba mai dorewa, da kuma neman sabuwar bunkasuwa ta hanyar hadin gwiwa”.
An gudanar da bikin ne a birnin Munich na kasar Jamus, inda aka gabatar da jerin ayyukan hadin gwiwa a bangaren yada labarai, da ayyukan fina-finai da sauransu. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp