Jiya Litinin, babban rukunin gidan rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG, da hadin gwiwar ofishin MDD dake Geneva, da ofishin dindindin na kasar Sin a MDD dake Geneva da sauran tawagogin wakilan hukumomin kasa da kasa dake Switzerland, sun gudanar da bikin murnar ranar harshen Sinanci ta MDD, da bikin nune-nunen shirye-shiryen bidiyo da talibjin na kasar Sin a ketare karo na 4, a harabar ofishin na MDD wato “Palace of nations” dake birnin Geneva.
Mataimakin shugaban sashen yayata ayyuka na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban CMG Shen Haixiong ya gabatar da jawabi yayin bikin. Kaza lika, babbar darektar ofishin MDD dake Geneva Tatiana Valovaya, da wakilin dindindin na kasar Sin a ofishin MDD dake Geneva da sauran hukumomin kasa da kasa Chen Xu, sun halarci taron tare da gabatar da jawabai.
- Kasar Sin Ta Bayyana Tarin Rarar Da Take Da Shi Ta Albarkartun Mai Da Iskar Gas
- Sin Ta Kalubalanci Amurka Da Ta Dubi Kanta Game Da Yanayin Kare Hakkin Dan Adam
A cikin jawabinsa, Shen Haixiong ya ce, bikin nune-nunen na wannan karo wanda CMG ya gabatar, na da taken “Kuzari”, wanda ya gayyaci abokan kasa da kasa da suke kaunar al’adun kasar Sin, don tattara kuzarin matasa, da mabambantan al’adu, da nufin kafa wata gada ta mu’ammala ta amfani da harshe da bidiyo. Yana mai fatan matasan kasa da kasa za su hada kai karkashin bikin, don fahimtar ainihin kasar Sin mai zamanintarwa daga dukkan fanonni.
A nata bangare, Tatiana Valovaya ta ce, an taru a wannan wuri ne don more mabambanta al’adun kasar Sin. Ta ce harshe ba hanyar mu’ammala ce kadai ba, ya kasance wata gada dake hada ilmi da al’umma tare. A yau, ana fahimtar dalilin da ya sa Sinanci ke jawo hankalin mutane, da ma karfi da yake bayyanawa. (Amina Xu)