Babban rukunin gidajen talibijin da rediyo na kasar Sin wato CMG ta hadin kai da gidan talibijin na “Silk Way” da na “Atameken” na kasar Kazakhstan da kuma yi hadin kai da kamfanin dillancin labarai na “Khovar” da gidan talibiji na “Sinamo” na kasar Tajikistan wajen gudanar da bikin nune-nunen shirye-shirye masu inganci na CMG a Astana fadar mulkin kasar Kazakhstan da Dushanbe, fadar mulkin kasar Tajikistan, a ran 30 ga watan da ya gabata, gabanin ziyarar aikin da shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai kasar, inda kuma zai halarci taro karo na 24 na majalisar shugabannin kasashe mambobin kungiyar hadin kai ta Shanghai wato SCO. A yayin bikin nune-nunen, an gabatar da shirye-shirye fiye da 10 ciki har da “Haduwa da Xi Jinping” ta wasu muhimman kafofin yaba labarai a kasar, ta yadda za a daukaka huldar kasashen biyu da ciyar da hadin kansu gaba.
Shugaban CMG Shen Haixiong a cikin jawabinsa ta kafar bidiyo ya ce, shirye-shiryen da za a gabatar musamman ma “Haduwa da Xi Jinping” da “Kiran Hanyar Siliki”, ba ma kawai suna bayyana al’adun kasar Sin ba, har ma da tushen muradun bai daya na Bil Adam, kuma ya yi imanin cewa shirye-shiryen za su samu karbuwa daga al’ummar kasashen biyu. Ya kara da cewa, CMG na fatan zurfafa hadin gwiwa da takwarorinsa na kasashen biyu don kara raya huldarta da kasashen biyu, kana da taka rawar gani wajen ingiza gina kyakkyawar makomar tsakaninta da kasashen biyu ta bai daya. (Amina Xu)