Yau Asabar, an gudanar da taron dandalin tattauna al’adu na kasa da kasa na Golden Panda na 2025 a birnin Chengdu. Li Shulei, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana ministan sashen fadakar da al’umma na kwamitin kolin JKS, ya halarta tare da sanar da bude taron.
Mahalarta na kasar Sin da na kasashen waje da suka halarci bikin bude taron sun bayyana cewa, ba za a iya raba tinkarar kalubale da samun kyakkyawar makoma, da karfin al’adu da wayewar kai ba. Sun jaddada muhimmancin zurfafa hadin giwwar al’adu na kasa da kasa a fannonin raya ilimi, kimiyya da fasaha, al’adu, da kafofin watsa labarai don kara inganta hadin kan al’adu da mu’ammalar jama’a.
Dandalin tattauna al’adu na kasa da kasa na Golden Panda na 2025, muhimmin bangare ne na bikin bayar da lambar yabo ta Golden Panda, ya jawo baki sama da 780 daga gida da waje don halartar taron.(Safiyah Ma)












