An gudanar da taro game da sana’ar sarrafa sinadarai na kasa da kasa karo na 12, kana da babban taron kawancen sana’ar karo na 21 na yankin Asiya da tekun Pacific wato WCCE12&APCChE2025 a nan birnin Beijing.
Taron na jiya Litinin mai taken “Kwaskwarimar da ake yi wa sana’ar sarrafa sinadarai don tinkarar kalubalen duniya”, ya jawo hankulan kwararrun masana kimiyya dake sahun gaba, da jagororin sana’ar da kusoshin kamfanoni da sauransu kimanin 5000 daga kasashen duniya 66.
Ban da wannan kuma, kamfanoni da hukumomi na kasa da kasa fiye da 130 sun halarci bikin. Yayin taron, Sin ta gabatar da rahotanni 2 game da nazarin da Sin take yi a bangaren fasahar makamashin hydrogen, a kokarin kafa misali a hukumance, ta yadda za a gaggauta samar da ma’aunin kimiyya a wannan fanni, da amfani da shi a mabambantan bangarori.
Dadin dadawa, an ce, Sin ta zama kasa mafi girma ta fuskar samar da kayayyaki bisa dogaro da sarrafa sinadarai da kuma amfani da su. Kasuwar Sin cike take da kuzari, inda matsakaicin karuwar yawan bukatunta a kowace shekara ta kai kashi 60 cikin kashi 100 kan na daukacin duniya, kasuwar da ta kara karfin daga matsayin sana’ar. Har ila yau, yawan kudaden da Sin ta samu a bangaren sarrafa sinadarai masu inganci, ya kai kashi 50 cikin kashi 100 kan na daukacin kasuwar duniya. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp