Jiya Litinin an gudanar da taron dandalin tattaunawa game da kirkire-kirkire na kafofin yada labaru na kasa da kasa karo na 3 a nan Beijing, fadar mulkin kasar Sin, wanda babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG ya shirya.
Taron wanda ya gudana a zahiri, da kuma ta kafar internet, ya hallara wakilai fiye da 200 daga kungiyoyin kasa da kasa, da manyan kafofin yada labaru na gida da wajen kasar Sin, da dandalolin kwararru, da manyan kamfanonin kasa da kasa. Kuma babban takensa shi ne “Yin amfani da kimiyya da fasaha don amfanar da jama’a, da kuma sauke nauyi tare, yayin da kafofin yada labaru suke amfani da fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam”.
Shugaban CMG Shen Haixiong, ya bayyana cikin jawabinsa cewa, ci gaban kirkire-kirkiren kimayya da fasaha, ya ba da jagoranci ga ci gaban wayewar kan dan Adam, da kuma haifar da rashin tabbas ga duniya mai sauye-sauye. Don haka dole ne a tsaya tsayin daka kan amfani da kimiyya da fasaha wajen amfanar da jama’a, ba tare da haifar da hadari ba, da kuma shigar da sassa daban daban don kulawa da su, a kokarin raya nagartacciyar fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam, mai sauke nauyi da kuma dorewa.
Yayin taron, Shen Haixiong da shugaban hadaddiyar kungiyar gidajen rediyon Afirka Grégoire Ndjaka, da wakilan kafofin yada labarun kasa da kasa, sun kaddamar da “Kiran ayyukan kafofin yada labaru dangane da kulawa da fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam”. (Tasallah Yuan)