An gudanar da taron hadin gwiwar kimiyya da fasaha da kirkire-kirkire na duniya mai taken “samun ci gaba ta hanyar kimiyya da fasaha da yin kirkire-kirkire” yau a nan birnin Beijing, inda shugabannin kasa da kasa, da na kungiyoyin kasa da kasa, da shahararrun masana kimiyya da kuma shugabannin rukunonin masana’antu da cinikayya suka halarci taron.
Mahalarta taron sun bayyana cewa, bangaren kimiyya da fasaha na kasar Sin, a ko da yaushe yana ba da shawarar bude kofa ga kasashen waje da yin hadin gwiwa da mu’amala a tsakanin kasa da kasa.
A yayin taron, shugaban kungiyar hadin gwiwar masana’antu da cinikayya ta kasar Sin, Gao Yunlong ya yi nuni da cewa, Sin ta aiwatar da shirin raya dangantakar abokantaka kan kimiyya da fasaha a tsakaninta da kasashe da yankuna fiye da 160. A nan gaba, Sin za ta kara bude kofa ga kasashen waje.
Mataimakin shugaban kasar Ghana Mahamudu Bawumia, ya yi imanin cewa, kimiyya da fasaha da yin kirkire-kirkire, su ne mabudin ci gaban zamantakewar al’umma.
Kana ya yi nuni da cewa, fasahohin sadarwar zamani, suna da muhimmanci sosai ga ci gaban nahiyar Afirka, ya kuma nuna godiya ga tallafin da kasar Sin take bayarwa a wannan fanni. (Zainab)