Da yammacin yau Talata ne aka gudanar da taron kolin ASEAN-Sin-GCC karo na farko a birnin Kuala Lumpur fadar mulkin kasar Malaysia. Inda a cikin jawabinsa na bude taron, firaministan kasar Malasiya Dato’ Seri Anwar bin Ibrahim, ya jadadda cewa, taron kolin na wannan karo da ya nuna hadin gwiwa tsakanin yankunan ya shiga wani sabon mataki, wanda ke da muhimmiyar ma’ana.
Anwar ya kara da cewa, kungiyar tarayyar kasashen kudu maso gabashin Asiya wato ASEAN, da Sin, da kuma kwamitin hadin gwiwar kasashen Larabawa na yankin Gulf wato GCC, jimillar al’ummunsu baki daya ta haura biliyan 2.1, kana yawan tattalin arzikinsu ya kai kusan dalar Amurka tiriliyan 25, kana suna da kyakyawar makomar hadin gwiwa.
Bugu da kari, ya yaba da gudummawar da Sin ta bayar a yayin hadin gwiwar ci gaban yankunan, tare da jadadda cewa, Sin abokiyar hadin gwiwa ce ta kasashen ASEAN cikin dogon lokaci, yayin da bangarorin biyu suka taka muhimmiyar rawa a fannonin sadarwa, da fasahohi, da ciniki da sauransu. Ya ce, taron kolin ya kafa wani sabon misali a fannin cimma nasarar hadin gwiwar kasashe masu tasowa.(Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp