Mataimakin firaministan kasar Sin kuma mai karban bakuncin taron tattaunawa kan tattalin arziki da hada-hadar kudi a tsakanin Sin da Birtaniya He Lifeng da ministar kudi ta kasar Birtaniya Rachel Reeves sun shugabanci taron tataunawar karo na 11 a nan birnin Beijing a yau.
He Lifeng ya bayyana cewa, Sin tana son yin kokari tare da Birtaniya wajen aiwatar da ayyukan da shugabannin kasashen biyu suka cimma daidaito a kai, da raya dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasashen biyu, da kara yin mu’amala da juna, da fadada hadin gwiwar tattalin arziki da hada-hadar kudi a tsakaninsu don kara samar da kuzari ga raya dangantakar dake tsakanin Sin da Birtaniya mai moriyar juna yadda ya kamata.
- Miji Da Mata Sun Samu karin Girma Zuwa Farfesa A BUK
- Xi Ya Yi Kira Da A Gudanar Da Aikin Tantance Harkar Kudade Mai Inganci Don Inganta Bunkasar Tattalin Arziki Da Zamantakewa
A nata bangare, Reeves ta bayyana cewa, kasar Birtaniya tana son kara yin hadin gwiwa tare da kasar Sin a fannin tattalin arziki da hada-hadar kudi, da ci gaba da raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu mai girmamawa juna na dogon lokaci.
A yayin taron tattaunawar, bangarorin biyu sun cimma daidaito kan jerin ayyukan samun moriyar juna. Kana He Lifeng da Reeves sun halarci taron koli na samar da hidimar hada-hadar kudi na Sin da Birtaniya karo na 4. (Zainab Zhang)