A daren ranar 6 ga wannan wata, an gudanar da wani biki mai taken “Bikin Bazara Namu” a cibiyar hukumar bunksa ilmi da kimiyya da fasaha da al’adu ta MDD, wato UNESCO dake birnin Paris na kasar Faransa, wanda babban rukunin Sin dake hukumar, da gidan talabijin na lardin Henan na kasar Sin suka karbi bakuncin gudanar da shi, don murnar cewa, Bikin Bazara na al’ummar kasar Sin ya shiga cikin jerin bukukuwan al’adun gargajiya da bil’adama ya yi gado a duniya.
Babbar wakiliyar Sin dake hukumar UNESCO, Yang Xinyu ta bayyana cewa, an yi wannan shagali ne don murnar bikin gargajiya na al’ummar kasar Sin don more al’adu tare da sassan duniya, da kara matsa kaimi ga yin hadin gwiwa da mu’amala da juna a fannin al’adu.
Direktar hukumar UNESCO, Audrey Azoulay ta bayyana ta kafar bidiyo cewa, a halin yanzu, Bikin Bazara ya kasance wani biki na duniya, wanda yake nuna kyakkyawan fata na jin dadin zaman rayuwa da zaman lafiya a dukkan duniya baki daya. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp