A yau Talata ne zaunannen kwamitin majalissar wakilan jama’ar kasar Sin ya kira taron, inda aka kada kuri’ar amincewa da Wang Yi a matsayin ministan harkokin wajen kasar, tare da Pan Gongsheng da aka nada a matsayin shugaban babban bankin kasar ta Sin. Kaza lika taron ya karbi kundin gyaran fuskar da aka yiwa dokar hukunta manyan laifuka.
Gyaran fuskar dokar dai ya ba da karfi ne ga bangarorin kyautata aiwatar da dokokin kwamitin kolin JKS, masu nasaba da yaki da cin hanci, da ba da kariya ga kamfanoni masu zaman kan su bisa doka.
Har ila yau, kundin ya tanaji sassan hukunta laifuka masu alaka da ba da rashawa, da cin hanci a tsakanin jami’an kamfanoni masu zaman kan su. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp