A ranar Talata ne aka gurfanar da Tukur Mamu, mai shiga tsakani, tsakanin gwamnatin tarayya da ‘yan ta’adda da suka yi garkuwa da fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a watan Maris din 2022, a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja.
Mamu, wanda shi ne mawallafin jaridar Desert Herald da ke Kaduna, ya ki amsa tuhumar da ake masa na tuhume-tuhume 10 da gwamnatin tarayya ta yi masa wadanda suka shafi daukar nauyin ta’addanci da dai sauransu.
Mawallafin, wanda ofishin babban lauyan gwamnatin tarayya (AGF) ya gurfanar dashi a gaban mai shari’a Inyang Ekwo na wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ya musanta kowacce irin alakarsa da ‘yan ta’addan.
Mai shari’a Nkeonye Maha na wata kotun tarayya a ranar 13 ga watan Satumba, 2022, ta baiwa hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) izinin tsare Mamu na tsawon kwanaki 60 domin baiwa DSS damar kammala bincike kan Mamu.
Ana zargin Mamu da karbar kudin fansar fasinjojin da ya kai kusan kudi dala 120,000.00 a madadin kungiyar ta’addanci ta Boko Haram daga iyalan wadanda aka yi garkuwa da su a harin jirgin kasan.