Wata kotu a yankin Gwagwalada a Abuja ta tsare wasu manoma uku a gidan gyaran hali bisa zargin yin garkuwa da wata mata.
Rundunar ‘yansandan ta gurfanar da Aminu Usman mai shekaru 26, Umar Salisu mai shekaru 25, Usman Umar mai shekaru 20, dukkansu mazauna kauyen Guys da ke Kwali a Abuja da laifin hada baki da kuma yin garkuwa.
- Zan Tabbatar Da An Yi Sahihin Zaben Da Ba A Taba Irinsa Ba – Buhari
- Tinubu Ya Godewa Buhari Kan Amincewa Da Kara Wa’adin Kwanakin Daina Karbar Tsoffin Kudade
Sai dai wadanda ake tuhumar sun musanta aikata laifin.
Alkalin kotun, Malam Abdullahi Abdulkarim, ya dage ci gaba da sauraren karar har zuwa ranar 15 ga watan Maris.
Lauyan masu shigar da kara, Dabo Yakubu, ya shaida wa kotun cewa wadanda ake tuhuma, Aminu Ali, ya kai rahoton lamarin a yankin Gwagwalada a ranar 8 ga watan Janairu.
Ya ce wadanda ake tuhumar sun hada baki ne wajen yin garkuwa da wata mata Fatima Bello zuwa wani waje.
Ya ce laifin ya ci karo da sashe na 97 da na 271 na kundin laifuffuka.