Gwamnatin Chadi ta ce an kashe mutane da dama bayan wasu mutane dauke da makamai, wadanda ake zargin ‘yan jam’iyyar adawa ta ‘Socialist Party without Borders’ ne suka kai wa hukumar tsaron kasar hari.
Ministan sadarwa Abderaman Koulamallah ya fada a ranar Talata cewa, hakan ya biyo bayan yunkurin kashe shugaban kotun kolin kasar, yana mai zargin sakataren kudi na jam’iyyar adawa ta ‘Socialist Party without Borders’ da hannu a shirin.
- Shirin Gwamnati Na Samar Da Mafi Karancin Albashi
- Wa’adin Da Gwamna Kano Ya Dauka Na Yi Wa Kwamishinoni Hisabi Ya Cika: Kila Wasu Za Su Karbi Littafinsu A Hannun Hagu
An kama jami’in jam’iyyar da ake zargi amma a ranar Talata, kuma ‘yan jam’iyyarsa sun ce “an kashe shi”.
Gwamnatin ta ce ta kama wasu da dama da suka kai harin, yayin da ake ci gaba da neman sauran amma kuma babu tabbas kan cewa an kama shugaban jam’iyyar, Yaya Dillo, amma a wani sako da ya wallafa a Facebook da safiyar Laraba, ya ce sojoji sun kewaye su.
Wannan na zuwa ne mako guda bayan da shugaban kotun kolin ya bayyana cewa an kai wa ofishinsa hari.
A halin yanzu jami’an tsaro na sintiri a titunan N’Djamena, yayin da al’ummar kasar suka shiga cikin fargaba.
A wani ci gaban labarin kuma, a ranar 6 ga watan Mayu ne za a gudanar da zaben shugaban kasar Chadin wanda zai kawo karshen mulkin soji na shekaru uku da aka soma bayan shugaba Mahamat Idriss Deby Itno ya hau karagar mulki bayan rasuwar mahaifinsa a shekarar 2021.
Shugaban hukumar zaben kasar Ahmed Bartchiret, ya bayyana muhimman ranakun da za a gudanar da zaben shugaban kasar a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Babban Birnin Kasar, N’Djamena, kamar yadda shafin intanet na Tchadinfos mai zaman kansa ya ruwaito.
Bartchiret ya jaddada muhimmancin gudanar da zaben kafin lokacin damina, inda ya bukaci abokan huldar fasaha da na kudi da su ba da hadin kai ga shirin zaben kasar.
Yayin da har yanzu shugaba Deby bai bayyana sake tsayawa takara ba a hukumance, ‘yan adawa sun bukaci da kada ya sake neman wani wa’adi.
Deby, mai shekaru 38, ya yi alkawarin shirya zabuka cikin watanni 18 bayan ya dare kan karagar mulki a watan Afrilun 2021.
Duk da haka, gwamnatinsa ta soji ta ci gaba da rike madafun iko, inda ta kara wa’adin mulkinta da karin watanni 18.