Jami’an tsaro sun hana ‘yan jarida shiga ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), inda ake tattara sakamakon zaben gwamna da na ‘yan majalisar dokokin jiha da aka karasa a Jihar Adamawa.
Jami’an tsaron sun shaida wa manema labarai cewa “An ba mu umarni daga sama, cewa kada mu kyale kowane dan jarida ya shiga, sai wanda aka tantance, saboda haka ba za a bari kowa ya shiga ba.
- Manoman Doya 100 A Jihar Nasarawa Suka Amfana Da Horon Cibiyar NEPC
- Peng Liyuan Ta Gana Da Uwargidan Shugaban Brazil
“Babu wani dan jarida da zai shiga sai wanda aka tantance, shi ne umarnin da aka ba mu daga sama” in ji jami’an ‘yan sandan.
Dama dai akwai bayanai da ke yawo a jihar cewa akwai wasu mutane da suke ganin ko za ayi kare-jini biri-jini sai sun cimma manufarsu ta siyasa a lokacin zaben.
Lamarin da ya sa kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar PDP a jihar, nuna damuwa kan cewa ba zai amince da duk wani matakin da zai yi kazalandan ga bayyana sakamakon zaben.
A kwanan baya ne wani sakon muryar kwamishinan hukumar zabe ta jihar Barista Hudu Yunusa Ari, yana ba da umrni ga baturen zabe na karamar hukumar Fufore, da ke cewa “A taimaki matanen nan” da ya ke ita ce kawai mace guda da ta tsaya zabe.
Daga baya hukumar zaben ta ayyana zaben da cewa bai kammala ba, duk da dan takarar jam’iyyar PDP, gwamna Ahamdu Umaru Fintiri, na kan gaba ga ‘yar takarar jam’iyyar APC, Aishatu Dahiru Ahmad Binani, da kuri’u sama da dubu 31.
Rahotanni dai na nuni da cewa INEC, za ta sauya wurin da ta ke tattara sakamakon zaben zuwa wani wajen da ba a kai ga tantancewa ba zuwa lokacin hada wannan rahoton.