Jami’an rundunar ‘yansandan Nijeriya sun bindige wani “Shahararren mai garkuwa da mutane” da ya addabi yankin babban birnin tarayya Abuja.
An kashe fitaccen dan fashin mai suna Isa Dei-Dei ne a yayin wani artabu da jami’an tsaron da suka fatattaki maboyar masu garkuwa da mutanen wadanda suke yin barazana ga mazauna yankin.
- Za Mu Tabbatar Kotu Ta Hukunta Dakataccen Kwamishinan Zaben Adamawa Hudu Ari -Fintiri
- Falana Ya Kai Karar Gwamnatin Tarayya Da Jihohi Kan Yara Da Ba Su Zuwa Makaranta
Olumuyiwa Adejobi, kakakin rundunar ‘yansandan wanda ya bayyana hakan a safiyar ranar Laraba, ya bayyana cewa, sauran ‘yan ta’addan sun gudu a lokacin da suka ga ‘yansandan amma sun tsira da kyar da harbin bindiga.
Adejobi, mataimakin kwamishinan ‘yansandan, ya roki jama’a musamman ma’aikatan lafiya da su yi gaggawar kai rahoton duk wanda aka gani da raunin harbin bindiga domin cafke sauran miyagun.