Kimanin ‘ya’yan kutare da guragu guda 24 aka horas akan koyon sana’oin hannu daban-daban a jihar Sokoto.
Wata kungiyar da ke tallafawa kutare ta Leprosy Mission Nigeria (TLMN) ce, ta horar da ‘ya’yan masu bukata ta musanman don tallafawa Iyayensu.
- ‘Yan Fashin Daji Sun Kashe Mutum 4, Da Sace 18 A Harin Da Suka Kai A Wani Kauye A Sokoto
- Gwamnatin Sokoto Za Ta Kashe Biliyan 20.3 Domin Sayen Abinci Da Wasu Ayyuka
An zabo wadanda suka amfana da horon ne daga yankunan da suka hada da Gwadabawa, Sabon-gandi, Kara, da kuma Amanawa.
An horar da su ne kan koyon sana’oin hannu kamar dinkin keke, walda, kanikanci, kafintanci da zane-zane a kwamfuta.
Daraktan kungiyar, Mista Sunday Udo, a cikin jawabinsa a wajen taron ya sanar da cewa, an kaddamar da irin wannan bayar da horon a jihohi hudu a karkashin aikin taimakawa masu bukata ta musamman.
Shugaban sasaahen gudanar da mulki da inganta rayuwa na kungiyar Orowo Stephen ne ya wakilici Udo a wajen haron.
Kazalika Udo ya ce, masu dauke da larurar kuturtar na ci gaba da fusakantar wariya a cikin al’umar da suke zaune da su, inda ya kara da cewa, kungiyar za ta basu horon ne don suma su zama masu dogaro da kansu, maimakon dogara akan yin barace-barace a tituna.
Shi kuwa Dakta Kabiru Garba, wanda ya wakilci mataimakin gwamnan jihar a wajen horon, ya yabawa kungiyar akan wannan kokarin nata.
Ya ce, gwamnatin jihar ta mayar da hankali wajen inganta jin dadi da walwalar daukacin masu bukata ta musamman da ke a cikin jihar.
Garba ya bayyana cewa, gwamnatin jihar ta kirkiro da shirin tallafawa masu bukata ta musamman a jihar ta hanyar bai wa kownnensu tallafin naira 5,000 a duk wata.