Kasar Sin ta ja hankalin jama’a yayin kaddamar da bikin nune-nunen ayyukan gona da kiwon dabbobi na kasa da kasa na 2025 na Abidjan wato SARA, wanda ke mayar da hankali kan dabarun sarrafa amfanin gona domin cimma cikakken iko kan tsare-tsaren da suka shafi samar da abinci da zamanintar da aikin gona a nahiyar Afrika.
Firaministan Cote d’Ivoire Robert Beugre Mambe, ya bayyana yayin kaddamar da bikin a ranar Talata cewa, suna farin cikin karbar bakuncin kasar Sin, wadda kwarewarta a fannin aikin gona ya sa ta zama abar koyi.
- Hamas Za Ta Saki Dukkan Fursunonin Isra’ila Da Ke Hannunta
- Hisbah Ta Haramta Gidajen Casun Dare A Katsina
A cewarsa, an ayyana kasar Sin a matsayin babbar bakuwa a bikin SARA na wannan karo ne saboda yadda take jagorantar ayyukan gona a duniya da kyakkyawar dangantakar dake tsakaninta da Cote d’Ivoire.
Shi kuwa ministan kula da aikin gona na kasar Kobenan Koussi Adjoumani cewa ya yi, kasar Sin daya ce daga cikin mafiya samar da amfanin gona a duniya, kuma tana gabatar da gogewarta da ma damarmakin kasuwanci da take da su ga Cote d’Ivoire.
Za a kaddamar da bikin SARA karo na 7 a hukumance, daga ranar 7 ga watan Mayu zuwa 1 ga watan Yuni, a cibiyar nune-nune ta Abidjan. Bikin mai taken “me cikakken iko kan tsare-tsaren samar da abinci ke nufi ga nahiyar Afrika?” zai samu masu baje hajoji kimanin 800. (Mai Fassara: Fa’iza Mustapha)