Jami’an gwamnatin kasar Senegal da wakilan ‘yan kasuwar kasar, sun yabawa gudummawar kamfanonin kasar Sin a fannin bunkasa ci gaban masana’antun kasar, da ma kara farfado da tattalin arzikin kasar.
Sassan sun bayyana hakan ne yayin wani dandali da aka shirya, dangane da jarin da kamfanonin kasar Sin suka zuba a Senegal. An gudanar da dandalin ne a jiya Laraba a birnin Diamniadio, mai nisan kilomita kusan 40 daga kudu maso gabashin birnin Dakar fadar mulkin kasar.
Dandalin ya samu halartar sama da mutane 300, ciki har da jami’an gwamnatin Senegal, da wakilai daga sama da kamfanonin Sin da Senegal 150, da wakilan kungiyoyin ‘yan kasuwa, ya kuma kasance bangare na babban dandalin zuba jari na Senegal na shekarar 2025. (Mai fassara: Saminu Alhassan)