An bude atisayen soja kan teku bisa hadin gwiwar wasu kasashe a birnin Karachi na kasar Pakistan, a ranar 7 ga wata.
Asitayen sojan da kasar Pakistan ta tsara ya samu halartar jiragen ruwan soja daga kasashe sama da guda 10, wadanda suka hada da Sin, da Indonesiya, da Japan, da Italiya, da Malasiya, da kuma Amurka da dai sauransu. Haka kuma, sauran kasashe sama da guda 40 sun tura masu sa ido wajen atisayen.
An raba atisayen sojan zuwa matakai guda biyu. Mataki na farko shi ne tsakanin ranaku 7 zuwa 9 ga watan Fabrairu, inda za a yi atisayen soja kan tashar jiragen ruwa, da tattaunawa kan atisayen, da tattaunawa kan ayyukan musamman tsakanin bangarori daban daban da dai sauran ayyuka. Sa’an nan, a tsakanin ranaku 10 zuwa 11 ga watan Fabrairu, za a fara mataki na gaba, wato atisayen soja kan teku, inda za a gudanar da atisaye a kan teku, da aikin binciken jiragen ruwan soja na kasa da kasa. Kana, mahalartar atisayen za su gudanar da ayyukan samar da kayayyaki da abubuwan da sojojin ruwa ke bukata, da kuma hadin gwiwa wajen yaki da ‘yan fashin teku da dai sauran ayyuka. (Mai Fassara: Maryam Yang)