Yau Laraba, aka kaddamar da bikin nune-nunen harkokin rediyo da fina-finai da talabijin na kasa da kasa na Beijing karo na 32 ko kuma BIRTV2025 a Beijing, fadar mulkin kasar Sin, wanda kamfanin CBIC na kasar Sin ya dauki nauyin shiryawa, bisa jagorancin babbar hukumar kula da harkokin rediyo da talabijin ta kasa gami da babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasa wato CMG.
Bikin na BIRTV2025 yana kokarin kafa wata gada don inganta mu’amala tsakanin kasa da kasa ta hanyar gudanar da harkokin kasa da kasa, ciki har da taron sanin makamar aiki don inganta kwarewar kafafen yada labaran Sin da Afirka, wanda zai mayar da hankali kan irin labaran da suka kamata a watsa, gami da hanyoyin watsa su, tare kuma da lalubo sabbin hanyoyin hadin-gwiwar Sin da Afirka a fannin masana’antun talabijin da rediyo.
Bikin BIRTV2025 na bana wanda za’a rufe shi a ranar 26 ga wata, ya samu halartar kamfanoni sama da 500 daga kasashe da yankuna fiye da 20, wadanda suke nuna sabbin nasarori da fasahohin da suke da su a sana’o’in da suka shafi rediyo da fina-finai da talabijin da kuma intanet. (Murtala Zhang)












