Yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke shirin kai ziyara kasar Hungary, a yau Litinin babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, da gidan talabijin na ATV dake Hungary, sun kaddamar da bikin nuna wasan kwaikwayon kasar Sin a birnin Budapest, fadar mulkin kasar Hungary, inda za a nuna wasannin kwaikwayo da fina finai masu kwarkwatar ido fiye da 10, da CMG ya gabatar ga kafofin watsa labarai na Hungary.
A gun bikin, shugaban CMG Shen Haixiong, ya gabatar da jawabi ta bidiyo, inda ya ce CMG yana sa ran yin kokari tare da bangarorin Hungary daban daban, wajen ba da gudummawar zurfafa dangantakar hadin gwiwa tsakanin Sin da Hungary bisa manyan tsare-tsare kuma daga duk fannoni. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp