Bisa ga yadda wasu fina-finan kasar Sin ke samun karbuwa a kasuwannin kasa da kasa, ciki har da fim din “Ne Zha 2”, a yau Litinin an kaddamar da bikin “Tafiya a kasar Sin bisa fina-finan kasar” a gidan tarihi na fina-finai na kasar Sin dake nan birnin Beijing, wanda hukumar kula da fina-finai ta kasar Sin da babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) suka shirya, kuma gidan talabijin na kasa da kasa na kasar Sin (CGTN) da cibiyar shirye-shirye ta tashar fina-finai suka karbi bakuncinsa.
Bikin wanda ya fi mayar da hankali kan gudanar da ayyukan tallata fina-finai da yawon shakatawa ta hanyar nuna fina-finan kasar Sin a ketare, da shirya bikin nune-nunen fina-finan kasar Sin a ketare, da kuma bikin nune-nunen fina-finai na cikin gida da na ketare, yana neman fadakar da masu kallon fina-finai na ketare a kan yanayin kasar Sin, tare kuma da jawo masu yawon shakatawa na ketare su zo kasar Sin don kara fahimtar kasar. (Mai fassara Bilkisu)