ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, June 13, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnati Ta Buƙaci Sauƙaƙa Tsarin Samar Da Biza Don ƙarfafa Kasuwancin ‘Yan Nijeriya A Duniya

by Sulaiman
1 year ago
Biza

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya buƙaci ƙasashen duniya da su sauƙaƙa tsarin ba da biza ga kamfanonin Nijeriya da ke ƙoƙarin kafa masana’antu da kasuwanci a ƙetare.  

Ministan ya yi wannan kira ne a Addis Ababa, babban birnin Habasha, a ranar Lahadi yayin da yake wakiltar Shugaban Ƙasa Bola Tinubu a taron shugabannin ƙasashen Afirka karo na 38 da Majalisar Tarayyar Afirka (AU) ta shirya.

ADVERTISEMENT
  • Gwamnan Kano Ya Gargaɗi Malamai Kan Sa Yara Aikin Wahala
  • Ƴan Nijeriya 85 Za Su Iso Lagos Daga Amurka A Yau

A yayin wata ganawa da shugabannin al’ummar Nijeriya da ke Habasha, Idris ya jaddada cewa Nijeriya na samar da kyakkyawan yanayi ga kamfanonin ƙasashen waje don su zuba jari a cikin ƙasar, don haka ya dace a samar da irin wannan dama ga ‘yan kasuwar Nijeriya a ƙasashen waje.

LABARAI MASU NASABA

Gwamnonin Arewa-maso-yamma Sun Kaddamar Da Shirin Rage Radadin Talauci A Yankin

Sake Jan Damarar Soja Da Japan Ke Yi Karin Alama Ce Mai Hadari

Ya ce: “A bara, na wakilci Nijeriya a Indonesiya, kuma na gano cewa akwai manyan kamfanoni hamsin daga Indonesiya da ke aiki a Nijeriya, amma ba mu da ko kamfanoni biyar daga Nijeriya da ke aiki a Indonesiya.

“Idan suna son zuwa ƙasar mu su yi kasuwanci saboda yawan mutanen mu da kuma damar da muke da ita na sayen kayayyakin su da ayyukan su, to ya kamata a samar da tsarin da zai ba da dama ga kamfanonin Nijeriya su ma. Matsalar ba da biza ga ‘yan Nijeriya na nan a Indonesiya da Habasha.”

Dangane da matsalar da ‘yan Nijeriya ke fuskanta bayan da gwamnatin Habasha ta soke tsarin nan na ‘e-visa’ da ‘Visa-on-Arrival’ ga matafiya daga Nijeriya, Idris ya tabbatar da cewa za a ɗauki matakin diflomasiyya ta hannun Ministan Harkokin Waje don magance matsalar.

Ministan ya bayyana cewa manufofin ba da biza a tsakanin ƙasashe na tafiya ne bisa tsarin da ke bai wa kowanne ɓangare dama daidai.

Ya ce ya zama dole ƙasashe su kasance masu adalci wajen aiwatar da manufofin da za su amfanar da ‘yan ƙasar su da na ƙasashen da suke hulɗa da su.

Ya ce: “Duk wata dangantaka da ƙasashen waje tana tafiya ne bisa tsarin amfanin juna. Idan muna ba su ‘Visa-on-Arrival’, babu dalilin da zai sa su hana mu ‘Visa-on-Arrival’.”

Ministan ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da ke zaune a ƙasashen waje da su kasance jakadu nagari, su nuna halaye nagari domin inganta sunan ƙasar.

“Ba ma yarda da mutanen da za su ɓata mana suna. Kuna da rawar da za ku taka, saboda ku ne ke zaune a nan. Idan ba ku wakilce mu da kyau ba, ba za a girmama mu ba. Ba wai ziyarar Shugaba Tinubu ko wani minista ce za ta gyara abin ba, amma ‘yan Nijeriya da ke zaune a nan ne za su iya gyara yadda duniya ke kallon ƙasar mu,” inji shi.

Idris ya kuma yi bayani kan sababbin manufofin da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa, inda ya ce an samu cigaba mai kyau a fannin farfaɗo da tattalin arziki, inganta ababen more rayuwa, yaƙi da rashin tsaro, da kuma dawo da ƙwarin gwiwar masu zuba jari a Nijeriya.

Ya ce Nijeriya ta samu jarin ƙetare na kusan dala biliyan 1.07 don kafa masana’antu da za su ƙera magunguna, matakin da zai taimaka wajen bunƙasa masana’antar magunguna a ƙasar, samar da ayyukan yi, da kuma ƙarfafa ɓangaren kiwon lafiya.

Haka nan, Ministan ya bayyana cewa a cikin kwanaki ƙasa da 250, an raba sama da naira biliyan 32 ga ɗalibai ƙarƙashin Shirin Lamunin Ɗalibai, domin tabbatar da cewa kowa na samun damar karatun boko ba tare da matsalar rashin kuɗi ba.

Dangane da ƙoƙarin yaƙi da rashin tsaro, Idris ya ce a shekarar 2024 kaɗai, jami’an tsaro sun kashe ‘yan ta’adda da ‘yan fashi 8,000, sun ceto mutane 8,000 da aka yi garkuwa da su, tare da cafke mutane 11,600 da ake zargi da aikata laifuka.

Har ila yau, ya tabbatar da cewa an kawar da ‘yan ta’adda daga hanyar Kaduna zuwa Abuja, wadda a da wurin aikata miyagun laifuka ce, lamarin da ya kawo sauƙi ga matafiya.

Da yake jawabi, Shugaban Al’ummar Nijeriya da ke Habasha, Muideen Alimi, ya ce suna shirin yin haɗin gwiwa da Hukumar Kula da ‘Yan Nijeriya Mazauna Ƙetare (NIDCOM) don shirya taron tattaunawa kan bunƙasa tattalin arziki ta hanyar kasuwanci tsakanin ƙasashen Afirka.

Ya buƙaci Nijeriya da ta goyi bayan shirin samar da Babban Bankin Afirka, tare da tabbatar da cewa Nijeriya ta taka muhimmiyar rawa a Hukumar Harhaɗa Kuɗaɗen Afirka (African Remittance Agency).

Taron ya samu halartar Darakta Janar ta Hukumar NIDCOM, Abike Dabiri-Erewa, da wasu manyan jami’an gwamnati.

Biza
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Muhallin Halittu Da Aka Yi Gado A Kasar Sin Sun Samu Ci Gaba Ta Fuskar Ba Su Kariya
  • Sulaiman
    Sake Jan Damarar Soja Da Japan Ke Yi Karin Alama Ce Mai Hadari
  • Sulaiman
    Shugaban Majalisar Bayar Da Shawara Kan Harkokin Siyasa Ta Kasar Sin Ya Yi Kira Da A Raya Dangantakar Gabobi Biyu Na Mashigin Tekun Taiwan Cikin Lumana
  • Sulaiman
    Sin Ta Zama Abin Koyi Na Sauyi Da Ci Gaba Ga Kasashe Da Dama, In Ji Shalva Papuashvili

MASU ALAKA

Gwamnonin Arewa-maso-yamma Sun Kaddamar Da Shirin Rage Radadin Talauci A Yankin
Rahotonni

Gwamnonin Arewa-maso-yamma Sun Kaddamar Da Shirin Rage Radadin Talauci A Yankin

June 13, 2026
Labarai

Next Post
Yawan Tikitin Kallon Fim Din “Ne Zha 2” Da Aka Sayar a Karshen Mako Ya Shiga Sahun Gaba Na Fina-Finai 5 A Arewacin Amurka

Yawan Tikitin Kallon Fim Din “Ne Zha 2” Da Aka Sayar a Karshen Mako Ya Shiga Sahun Gaba Na Fina-Finai 5 A Arewacin Amurka

LABARAI MASU NASABA

Muhallin Halittu Da Aka Yi Gado A Kasar Sin Sun Samu Ci Gaba Ta Fuskar Ba Su Kariya

Muhallin Halittu Da Aka Yi Gado A Kasar Sin Sun Samu Ci Gaba Ta Fuskar Ba Su Kariya

June 13, 2026
Gwamnonin Arewa-maso-yamma Sun Kaddamar Da Shirin Rage Radadin Talauci A Yankin

Gwamnonin Arewa-maso-yamma Sun Kaddamar Da Shirin Rage Radadin Talauci A Yankin

June 13, 2026

Sake Jan Damarar Soja Da Japan Ke Yi Karin Alama Ce Mai Hadari

June 13, 2026
NANS Ta Kafa Kwamitin Ganin Yadda Ake Tafiyar Da Ayyukan TETFund

NANS Ta Kafa Kwamitin Ganin Yadda Ake Tafiyar Da Ayyukan TETFund

June 13, 2026
Shugaban Majalisar Bayar Da Shawara Kan Harkokin Siyasa Ta Kasar Sin Ya Yi Kira Da A Raya Dangantakar Gabobi Biyu Na Mashigin Tekun Taiwan Cikin Lumana

Shugaban Majalisar Bayar Da Shawara Kan Harkokin Siyasa Ta Kasar Sin Ya Yi Kira Da A Raya Dangantakar Gabobi Biyu Na Mashigin Tekun Taiwan Cikin Lumana

June 13, 2026
Ghana Za Ta Kai Ƙarar Canada Kotu Kan Hana Thomas Partey Shiga Ƙasar

Ghana Za Ta Kai Ƙarar Canada Kotu Kan Hana Thomas Partey Shiga Ƙasar

June 13, 2026
Sin Ta Zama Abin Koyi Na Sauyi Da Ci Gaba Ga Kasashe Da Dama, In Ji Shalva Papuashvili

Sin Ta Zama Abin Koyi Na Sauyi Da Ci Gaba Ga Kasashe Da Dama, In Ji Shalva Papuashvili

June 13, 2026
Garkuwa Da Mutane Na Barazana Ga Dalibai Miliyan 1.9 Masu Jarrabawar WAEC A Sassan Nijeriya

Garkuwa Da Mutane Na Barazana Ga Dalibai Miliyan 1.9 Masu Jarrabawar WAEC A Sassan Nijeriya

June 13, 2026
Kasar Sin Na Adawa Da Matakin Amurka Na Amfani Da Tsaron Kasa Wajen Danne Wasu Kamfanonin Sinawa

Kasar Sin Na Adawa Da Matakin Amurka Na Amfani Da Tsaron Kasa Wajen Danne Wasu Kamfanonin Sinawa

June 13, 2026
‘Yansanda Sun Ceto Mutum 21 Da Aka Sace, Sun Kwato N4.8m Kuɗin Fansa

’Yansanda Sun Ceto Yaro Mai Shekara Shida Da Aka Sace, Sun Cafke Wanda Ake Zargi A Borno

June 13, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.