A ranar Juma’a 7 ga wata ne aka kaddamar da cibiyar koyon ilimin fasahar zamani ta Sin da Afirka a jami’ar karatu daga gida ta kasar Kenya da ke yankin birnin fasaha na Konza, mai tazarar kilomita 65 daga kudu maso gabashin Nairobi, babban birnin kasar Kenya.
Malaman jami’o’i daga jami’ar ta karatu daga gida ta kasar Kenya da jami’ar Donghua ta kasar Sin, sun halarci bikin kafa cibiyar ta koyar da ilimin fasahar zamani ta hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka da kuma cibiyar koyarwa daga gida ta jami’ar kasar Sin.
- Thomas Bach Ya Bai Wa Cmg Izinin Sarrafa Watsa Labarun Gasar Olympics Ta Lokacin Hunturu Ta Milan Ta 2026
- Amurka Ta Tasa Keyar Indiyawa Kusan 100 Zuwa Gida
Da yake jawabi, mataimakin shugaban jami’ar karatu daga gida ta kasar Kenya, Iliya Omwenga ya ce kaddamar da cibiyar ta bunkasa fasahar zamani, ta nuna wani muhimmin ci gaba a hadin gwiwar Sin da Afirka ta fannin ilimi.
Shi kuwa darektan ofishin hadin gwiwar kasa da kasa na jami’ar Donghua, Zhao Mingwei, cewa ya yi, kaddamar da cibiyar koyor da fasahar ta zamani ta kara tabbatar da muhimmancin hadin gwiwar Sin da Afirka a fannin ilimi da bunkasa fasahohi.
Zhao Mingwei ya kara da cewa, abokan hulda na kasar Sin da na Afirka sun daidaita sahu ta fuskar kokarin da suke yi wajen samun nasarar juyin juya halin ci gaban masana’antu kashi na hudu, wanda ke wajabta bukatar yin hadin gwiwa a aikace don karfafa manyan masu ruwa da tsaki da ke taka rawa a fannin tattalin arzikin fasahar zamani kamar matasa. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
ranar Juma’a 7 ga wata ne aka kaddamar da cibiyar koyon ilimin fasahar zamani ta Sin da Afirka a jami’ar karatu daga gida ta kasar Kenya da ke yankin birnin fasaha na Konza, mai tazarar kilomita 65 daga kudu maso gabashin Nairobi, babban birnin kasar Kenya.