Za a gudanar da dandalin Bo’ao na nahiyar Asiya daga gobe Talata zuwa ranar Juma’a 29 ga watan da muke ciki, a garin Bo’ao na lardin Hainan dake kudancin kasar Sin.
Taken dandalin na bana shi ne “Asiya da duniya: Fuskantar da kalubaloli da sauke nauyin bai daya”. Za a kebe bangarorin tattaunawa hudu, wato na tattalin arzikin duniya, da kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha, da bunkasuwar al’umma, da kuma hadin gwiwar kasa da kasa, kuma a karkashinsu, za a gabatar da kananan bukukuwan tattaunawa fiye da 40.
Da yammacin yau Litinin ne an kaddamar da cibiyar yada labarai ta dandalin, inda tuni aka shirya tsaf don gudanar da shi. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp