Hukumar kula da ayyukan ‘Yansanda (PSC) ta tsayar da ranar 16 ga Afrilu, 2024, don tantance lafiyar masu neman aikin da za a dauka a matsayin jami’an ‘yansanda.
Hakan ya fito ne cikin wata sanarwa da kakakin hukumar PSC, Ikechukwu Ani, ya fitar a ranar Litinin.
- Ma’aikatar Kudin Kasar Sin Ta Tsara Matakan Ingiza Ci Gaba Mai Inganci A Shekarar 2024
- Kasar Sin Na Maraba Da Abokai ‘Yan Kasuwa Daga Kasashe Daban Daban Da Su Ci Gaba Da Zuba Jari A Kasar
Ani ya ce, an zabi ranar 16 ga Afrilu ne domin ba wa masu neman aikin daga cikin musulmai damar kammala azumin watan Ramadan da kuma lokacin Lenten na Kirista da kuma baiwa duk ma’abota addini hakkinsu.
Ana sa ran tantancewar, za ta lashe tsawon makonni biyu ana gudanarwa, kuma wannan shi ke nuna cewa an kammala ayyukan cikin nasara.
Talla